Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Ta Lashi Takobin Samoshi


Real Madrid
Real Madrid

Kan batun sayen mai tsaron raga na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, David de Gea, mai shekaru 27, da haihuwa da kungiyar Real Madrid take bukatar saye, wakilin dan wasan Jorge Mendes, ya ce shi yake kawo cikas kan batun.

Jorge Mendes wanda har ila shine wakilin shahararen dan wasan kwallon kafa nan na duniya dan kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya ce shine ya sayar da Ronaldo, wa kungiyar Real Madrid a shekarun baya amman a yanzu dan wasan baya jin dadin zama a kungiyar ta Real.

Don haka nema harya yanzu cinikin David de Gea bai kammalu ba ,

A shekara ta 2015 kungiyar ta Real Madrid, tayi yunkurin sayen dan wasan amma abun yaci tura, inda yanzu ta raba hanun kan masu tsaron raga uku David de Gea, da Kepa Arrizabalaga na Athletic Bilbao, da kuma Courtois na Chelsea, kungiyar tace zatayi iya kokarinta wajan ganin ta dauko guda daga cikinsu a watan Janairu da zaran an bude hada hadar ‘yan wasa.

David de Gea yanzu tauraronsa tana haskakawa a kungiyasa ta Manchester United, inda ya yi tsaron raga a wasanin 12,amma ba a Zurara masa kwallo a raga ba a wasani daban daban da ya kama. wa kungiyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG