Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Best Buy Ya Yunkuro Taimakawa 'Ya'yan Marasa Galihu


Best Buy

Kamfanin sayarda da kayayyakin laturoni na Best Buy, da hadin gwiwar wata kungiyar mai zaman kanta Brian Coyle, ya bude wata cibiyar fasaha a Minneapolis, inda ake koyawa matasa ‘ya ‘yan bakin haure da marasa galihu ilimin yadda ake sarrafa kwamfuta.

Kamfanin ya shirya bude irin wadanna cibiyoyi har guda sittin a fadin Amurka domin taimakawa ‘ya’yan marasa galihu daga nan zuwa shekara 2020.

Shugaban kamfanin mai kula da aiyuka Trish Walker, yace makasudin wannan shirin shine domin horar da matasa miliyan daya kowace shekara da ilimin fasaha tayarda zasu iya samun guraben aiyuka da fasahar zamani.

Mr. Walker, ya kara da cewa za a horar da matasan a fannoni daban daban kamar na harkar kwamfuta da masu hada wake wake da kuma sana’ar dinki, wanda a cewar shugaban zai taimakawa matasan duk lokacin da suka fita neman aiki.

Abdirahman Mukhtar, daraktan shirin na horar da matasan ya ce cibiyar ta taimaka wajen baiwa matasan damar samun abin yi bayan sun tashi daga makaranta yarda zasu gujewa shiga rigima.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG