Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cigaban Duniya; Kimiyya Da Fasaha, Hadari Ga Yara A Gefe Daya


Asusun kula da jin dadin yara na Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyanar da irin alfanu da koma baya da yanar gizo ke haifarwa a wannan zamanin, musamman ga yara. A yayin kaddamar da rahoton UNICEF, aka bayyanar da hakan, da kuma wasu matakai don magance matsalar kimiyya da fasaha a duniya.

A cewar rahoton, daya cikin uku na mutane da ke amfani da yanar gizo a fadin duniya yara ne, duk da wannan karuwar, hukumar tace akwai karancin masaniya akan illar da hakan zai haifar, musamman ga lafiyar yaran.

Daraktan bincke da bayanai na kungiyar Mrs. Laurence Chandy, ta bayyana ma VOA cewar, cigaban yanar gizo ka iya zama wani abun sauyi ga rayuwar yara. “Muna da yakinin hakan musamman idan akayi la’akari da yaran dake rayuwa a inda babu irin damar, ko yara masu nakasa.

Rashin yanar gizo ka iya zama babbar matsala ga cigaban rayuwar su, haka ba zasu samu dama kamar ta sauran yara da suke a inda yanar gizo ke da saukin samu ba, Idan akayi la’akari da ‘yan shekarun baya, za’a ga cewar wannan babbar nasara ce musamman a irin cigaba da yara ke samu.

Haka kuma yanar kizo kan iya zama matsala ga rayuwar yara, wanda ya hada da amfani da bayanan yara ta hanyar da bai dace ba, yara kan samu damar kallon wasu abubuwan da basu kamata ba, haka da tauyema yara hakkin su ko zagin su ta amfani duk da yanar gizo.

Wasu kanyi amfani da shafufukan yanar gizo, wajen safarar yara, da satar su, kana da yi musu fayde duk ta kafar yanar gizo, hakan yasa hukumar damuwa da neman fito da sabon tsari, na yadda ya kamata iyaye su dinga kulawa da irin abubuwan da yaran su kanyi a yanar gizo.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG