Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaka Mai Manhajar Laturoni Bazata Shiga Jirgin Sama Ba


Jaka mai manhajar lataroni (Smart Suitcase) a turance, tana kara zama barazana ga wasu tashoshin jiragen sama. A ‘yan kwanakin baya ne, wasu tashoshin jiragen sama a fadin duniya, suka ayyanar da kudurin su, wanda ke cewar babu wani matafiyi da zai rike na’urar kwamfutar shi a yayin tafiya.

Ana su fahimtar suna ganin cewar tahaka ne kawai za’a iya magance matsalar ta’addanci a jiragen sama. Bayanai sun tabbatar da cewar jakar bata wuce kofofin tsaro na tashohin jirage, bisa dalilin ba’a iya kashe su, ko cire batirin su.

Rashin yin hakan zai sa baza a iya gano ko mutun na dauke da wasu abubuwan da suka saba dokokin kasa-da-kasa ba, kungiyar kamfanonin jiragen sama ta duniya sun bayyanar da cewar, zasu ba tashoshin jirage sabon tsarin tafiye-tafiye.

Su dai jakunkunan suna kunshe da na’urori da mutun zai iya cajin wayar shi, ko kuma kulle jakar tare da amfani da wayar hannu, jakar zata iya sanar da mutun inda yake, da kuma sanar da mutun hanyar da zaibi don zuwa wani guri da bai sani ba, tsarin GPS.

Wasu kamfanoni kamar su American Airlines, Delta da Alaska Airline, sun sanar da cewar daga ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 2018, zasu dinga umurtar matafiya da su dinga cire batirin jakar tasu mai latironi, kamin su tsallake bincike don shiga jirgin sama.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG