Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duncan Mighty Ya Ce Yana Da Alaka Da Matar Da Akai Zargi Da Sata


Fitaccen mawakin nan na jihar Fatakwal, Duncan Mighty, ya yi bayani akan matar nan da aka yi zargin ta yi sata a wani shago da kyammara ta dauka a satin da ya gabata.

Wani mai amfani da shafin facebook mai suna Ofon Le’cheery ne ya ska bidyon matar a satin da ya gabata inda ya rubuta cewa, “matar da ake tunani kannuwar fitaccen mawakin nan Duncan Mighty ce kyammara ta dauka yayin da take sata a kantin sayar da kaya”.

Kana ya kara da cewa “ta tabbatar da cewa ita kannuwar mawakin ce”

Mujallar Daily Post, ta wallafa cewa labarin ya yi ta yawo a yanar gizo, inda jama’a da dama masu kaunar mawakin ke mamakin yadda kanwar fitaccen mawaki zata yi sata.

Da yake mayar da martani akan bidiyon da yayi ta yawo a yanar gizo, mawakin ya bayyana cewa ‘yar uwarsa ce, sai dai ya bayyana cewa kusan shekara guda kenan da take fama da rashin lafiyar tabin hankali.

Ya bayyana cewa “wannan mata ce da aka kulle shagon ta sakamakon tabin hankali data samu tun shekarar data gabata, kuma ake mata magani a gida, amma satin daya gabata ta kubce daga gida kana lamarin ya auku a ranar Asabar data gabata”.

Duncan Mighty ya bayyana cewa yanzu haka shi ke daukar dawainiyar karatun dan cikin matar mai shekaru 15 da haihuwa, ya kuma taimakawa da dama daga iyalin da ta fito.

Daga karshe ya ce, yasan cewa watarana zata samu sauki.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG