Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sergio Aguero Ne Zai Yanke Hukunci Akan Kungiyar


Sergio Aguero
Sergio Aguero

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ce Sergio Aguero shi zai "yanke hukunci game da makomarsa" bayan ya ga dan wasan dan Kasar Argentina ya taimaka wa kungiyarsa ta doke Bournemouth.4-0 a gasar Firimiya lig mako na 19, Inda dan wasan ya jefa kwallaye 2, a ciki hudu da kungiyar ta Manchester City ta jefa a raga.

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tana zawarcin mai tsaron raga na PSG mai suna Kevin Trapp, mai shekaru 27, da haihuwa. Ita kuwa Manchester United ta saka fam miliyan £80 wajan ganin ta dauko dan wasan gaba na Monaco Thomas Lamer.

Lassana Diarra ya kammala kwangilarsa da kungiyar kwallon kafa ta Aljazira inda ya zu ya zamo mai cin gashin kansa watau (Free Agent) PSG dai ta nuna sha'awarta na ganin ta dauke dan wasan Lassana.

Arsenal ta nuna sha'awarta na ganin ta dauko Henrickh Mkhitaryan daga kungiyar Manchester United, ita kuwa Manchester United na zawarcin dan wasan tsakiya daga kungiyar Lazio mai suna Milinkovic Savic. Everton da Westham suna zawarcin dan wasan gaba na Celtic Moussa Dembele.

Chelsea tana zawarcin Wilfred Zaha dan shekaru 25, daga kungiyar Crystal palace, Stuttgart ta kammala sayen dan wasan gaba na Wolfsburg mai suna Mario Gomez, mai shekaru 32, a duniya

Inda zai rattaba hannu a watan Janairu da zaran an bude cinikayyar ‘yan wasa.

Real Madrid tana neman matashin dan wasan nan mai tsaron baya na Fulham Ryan Sessegnon mai shekaru 17, da haihuwa. Napoli tana neman mai tsaron raga na Manchester City Joe Hart.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG