Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Sun Yi Dumu-Dumu Wajan Saye Da Musayar Zaratan 'Yan Wasa


Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, ta kammala sayen dan wasan gaba na Hoffenheim, mai suna Sandro Wagner akan kudi yuro miliyan €13 na tsawon shekaru biyu da rabi 2020, kuma za a kammala yarjejeniyar a ranar 1/1/2018 da zarar an bude hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa.

kungiyar kwallon kafa ta Ajax, ta sallami mai horas da ‘yan wasanta Marcel Keizer, da mataimakinsa Dennis Beegkamp.

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Millan, na zawarcin danwasan tsakiya na Manchester united, Henrickh Mkhitaryan mai shekaru 28 da ya Koma kulob din a matsayin Aro a watan Janairu.

Mai horas da kungiyar Chelsea, Antonio Conte, ya ce yana bukatar kara karfi a kulob din don haka ya zamo dole zai nemo dan wasan gaba a watan Janairu mai zuwa. Mario Baloteli, mai shekaru 27 na shi'awar barin kungiyar Nice, Zuwa wata babban kulob kamar Manchester City ta kasar Ingila a matsayin kyauta.

Arsenal tana la'akarin ganin ta dauko dan wasan gefe na Barcelona Jose Arnaiz, dam shekaru 22 da haihuwa akan kudi fam miliyan 20. Liverpool ta jera sahu daya da Borussia Dortmund, wajan zawarcin dan wasan baya na Basel, Manuel Akanji.

Dan wasan tsakiya na Atletico Madrid, Nicolas Gaitan 29 na shirin barin kungiyar domin Komawa wani kulob a kasar Ingila a watan Janairu mai zuwa.

Newcastle na shi'awar dauko dan wasan Leicester city, Islam Slimani a watan Janairu da zarar an bude cinikaiyar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya.

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Alexsi Sanchez, na dab da cimma yarjejeniyar Komawa kungiyar Paris Saint-Germain.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG