Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tana Iya Yiwuwar Yafi Kowane Dan Kwallo Albashi


Harry Kane
Harry Kane

A cigaba da zawarcin ‘yan wasan kwallon Kafa da akeyi Mai horas da kungiyar kwallon Kafa ta Manchester United, Jose Mourinho na bukatar dauko dan wasan gefe na kungiyar PSG Lucas Moura a matsayin aro, Sai dai kungiyar ta PSG tace za su yarda ne kawai idan har ya kai ga dindindin a biya kimanin fam miliyan 40 nan gaba.

Tsohon dan wasan gaba na Liverpool John Aldridge yace yakamata Liverpool ta sayo dan wasan Arsenal Alexis Sanchez, akan kudi fam miliyan £40 domin ya maye gurbin Philippe Coutinho in har ya bar kungiyar ta Liverpool.

Manchester City ta fara tattaunawa da mai tsaron baya na Kungiyar Barcelona Samuel Umtiti kan batun kumawarsa kungiyar ta Manchester City,

Arsenal tana tattaunawa kan batun sayo dan wasan baya mai suna Konstantinos Mavropanos dan kasar Greece daga kungiyar PAS Giannina akan kudi fam miliyan £2.2. ta kuwa Inter Milan tana zawarcin dan wasan tsakiya na Manchester United Henrikh Mkhitaryan inda take shirin Sanya dan wasanta Joao Mario da suyi canji dashi cikin cinikin.

Har ila Yau Inter Milan tana neman Join Mata da ya dawo kungiyar da taka Leda daga Manchester United, Sai dai Manchester tana bukatar tsawaita kwangilar dan wasan nan gaba.

Tottenham tana shirin mayar da dan wasanta Harry Kane ya kasance dan wasan da yafi kowa daukan albashi a kasar Ingila bangaren Firimiya lig, inda zai karbi fam dubu £200 duk sati a matsayin albashi.

Kungiyar kwallon Kafa ta Manchester United na harsashen Jose Mourinho na iya barinta a karshen kakar wasan bana. Bayern Munich na nuna sha'awarta na zawarcin dan wasan tsakiya na Schalke Leon Goretzka, dan shekara 22, a duniya wanda Kungiyar Liverpool take cikin neman shi yanzu haka.

Sergio Aguero ya bada tabbacin zamansa a Manchester City har zuwa karewar kwangilarsa a sheharar 2020, ya kuma ce kungiyarce zata fadi makomarsa nan gaba.

Juventus na duba yuwar cigaba da ajiye dan wasan gefen ta Alex Sandro, a kungiyar bayan da Manchester United ta nuna sha'awarta na daukan dan wasan zuwa Old Trafford.

Crystal palace na tattaunawa da Kungiyar Lille kan mai tsaron bayanta Ibrahim Amadou mai shekaru 24, da haihuwa akan kudi fam miliyan £16.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG