Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Eden Hazard Real Madrid Ko Kuma Chelsea


Eden Hazard

Eden Hazard ya amince zai koma kungiyar Real Madrid daga Chelsea a karshe kakan wasan bana bayan da yaki amince wa da tayin da kungiyar sa ta Chelsea tayi masa.

Kwangilar dan wasan zai kare a Chelsea a shekarar 2020, har ila yau kungiyar ta Real Madrid tana zawarcin Mohammed Salah daga Liverpool, dan wasan dai ya kasance gwarzon dan wasan Africa 2017 da kuma na BBC duka a shekara daya inda a yanzu haka ya zurara kwallaye 18 a gasar Firimiya lig na Ingila.

Pierre-Emerick Aubameyang na shirin komawa kungiyar kwallon Kafar kasar Sin Guangzhou Evergrande, inda ake tsammanin zasu sayeshi kimanin fam miliyan £63.8 daga kungiyarsa ta Borussia Dortmund.

Kungiyoyi irin su Arsenal da Liverpool sun nuna sha’awarsu akan dan wasan.

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya bukaci matashin dan wasan Ajax Justin Kluivert, dan shekara 18, ya zauna a kungiyarsa na kasar Holland a wannan watan domin yana fatan kawo shi Ingila a farkon kakan wasan badi.

Kungiyar Barcelona tace har yanzu tana kan bakanta na sayo dan wasan gaba na Atletico Madrid Antoine Griezmann inda tace zata biya yuro miliyan €100 wajan sayen dan wasan kuma zata bashi daraja irin na manyan ‘yan kwallon da suke kungiyar irin su Messi da Luis Suarez.

Dan wasan baya na Chelsea Andreas Christensen ya sake rattaba hannu a kungiyar na tsawon shekaru hudu zuwa 2022, dan wasan wanda ya dawo daga aro na shekara biyu daga Borussia Monchengladbach, ya fafata wasannin 22 à wannan kakan wasannin na bana.

Arsenal tana zawarcin dan wasan tsakiya na Barcelona Rafinha dan wasan dai yana bukatar barin kungiyar ta Barcelona zuwa wata kungiyar da zai dinga samun kansa a cikin wasani.

Har ila yau kungiyar ta Arsenal tana neman dan wasan gaba na Bordeaux mai suna Malcom a shirin ta na maye gurbin Alexsi Sanchez wanda yake kokarin komawa Manchester City a watan nan.

Arsenal dai tana cikin jerin kungiyoyi uku na kasar Ingila da suke neman dan wasan wanda ya hada da Manchester United da kuma Tottenham.

Everton ta shiga sahun Southampton wajan zawarcin dan wasan gaba na Arsenal Theo Walcott 28, inda ta sa fam miliyan £20 kan sayen dan wasan a wannan watan na Janairu.

Arsenal ta biyo wata hanyar da zata samu damar tattauna da dan wasan tsakiyata Jack Wilshere, dan wasan mai shekaru 26 yana saran zai tattauna da kungiyar ta Arsenal a mako mai zuwa kan batun cigaba da zaman sa a kungiyar.

Tottenham ta dauko hanyar tattaunawa da dan wasanta Dele Alli mai shekaru 21,a duniya kan batun sabunta kwantiraginsa a kungiyar.

Manyan kungiyoyin Turai irin su Real Madrid da PSG tuni suka nuna sha'awarsu na sayen dan wasan kungiyar Anderlecht inda ta bukaci Manchester United ta biya fam miliyan £27 kan sayen dan wasan tsakiyata mai suna Leander Dendoncker.

Dan wasan tsakiya na Real Madrid Dani Ceballos mai shekaru 21 ya bukaci barin kungiyar don komawa kungiyar Liverpool ta kasar Ingila.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG