Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arsenal Zata Hukunta Alex Iwobi Idan Ta Same Shi Da Laifi


Kocin kungiyar kwallon kafa ta Araenal, Arsene Wenger, ya ce kungiyar zata hukunta dan wasanta Alex Iwobi, dan Najeriya, in har aka tabbatar yana cikin wadanda sukaje holewa (Party) sa'oi 36 kafin kungiyar ta fafata a wasan ta da Nottingham Forest a ranar lahadi inda aka doke Arsenal da ci 4-2.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Asabar an ga wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin sada zumunta wanda ya nuna dan wasan a gidan holewa yana rawa kafin wasansu na Kofin kalu bale FA Cup 2017/18 tsakanin Arsenal da Nottingham Forest. Kuma dan wasan ya buga wasa na mintoti 90 har aka tashi a wasan da kungiyar ta yi.

Kocin Arsenal, Wenger ya ce "ba zai yiwu ba" kuma "ba za'a amince da irin wannan dabi'a ba”, dan wasa ya fita cikin sa'o'i 48 kafin wasa kuma ya tafi (Party) ba.

Wenger, ya ce duk da kasancewar dan wasan ba'a same shi cikin wadanda suka sha barasa ba hakan ba zai hana a dauki mataki akan sa ba in har aka tabbabtar da faruwar lamarin. Kungiyar ta Arsenal, za ta duba irin hukuncin da ya dace da dan wasan Alex Iwobi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG