Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Mata Ta Kone Diyar Ta Kurmus Saboda Aure


A yau laraba ne jami'an 'yansanda a Pakisrtan suka bayyana cewa wata mata a kasar ta cinnawa diyarta wuta ta kone ta kurmus a sakamakon yanke shawarar auren wani mutum data zabawa kanta da diyar tayi.

Rahotannin sun bayyana cewa matashiyar mai suna Zeenat Bibi 'yar shekaru goma sha shidda ta hadu da ajalinta ne kwanaki kadan bayan an daura mata aure da mutumin da ta zabarwa kanta a gabashin birnin Lahore dake Pakistan.

Matar mai suna Perveen Bibi ta hallaka diyar tata Zeenat Bibi ne da misalin karfe tara na safe, babban jami'in jami'an 'yan sandan ya kara da cewa matashiyar ta auri wani mutum mai suna Hassan a ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata, kuma a cewar sa wannan shine karo na uku da irin wannan lamarin ke aukuwa a cikin watannin da suka shige wanda a ganinsu wata hanya ce ta "kisa a mutumce".

Haka ma a satin da ya gabata wata matashiya mai shekaru goma sha tara Maria Sadaqat ta sha azaba a hannun wasu gungun mutane sa'an nan suka cinna mata wuta a wani kauye dake kusa da babban birnin Islamabad a sakamakon kin amincewa da tayi ta auri wani dan abokin iyayen ta.

Akwai wata ma da ake tunanin shekarunta tsakanin goma sha shidda zuwa sha takwas da aka shake mata wuya sa'annan aka kone gangan jikinta a ranar 29 ga watan Afirilu, daga umurnin shugaban yankin kundumar Jirga dake yamma maso kudancin kasar domin zarginta da sa taimakawa kawarta tserewa da kuma auren wanda take so a boye.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG