Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kisan Na Ramuwar Gayya Ne


Hukumar liken asirin tsaron kasa ta DSS, a jihar Abia, ta nuna wasu matasa hudu ‘yan kungiyar asiri wadanda ake zargin su da kisan wasu ‘yan daliban jami’ar jihar Abia.

Daraktan hukumar a jihar Abia, K.S Kamoju, yace wadanda ake zargi an kama ‘yan kungiyar asiri ne da ake kira Burkina Faso, yana mai cewa wadanda ake zargin an kama su ne biyo bayan kisan da aka yiwa daliban jami’ar jihar.

Matasan da ake zargin Chikezie Macdonald, da shekaru 22, Chukwuemeka Awom, 25, Chodozie Obi, da Chigozie Francis Eberendu, 23, an kama sune a wurare daban daban.

Daraktan yace Macdonald, wanda aka fi sani da Starboy, dalibi ne a jami’ar aikin gona na Michael Okpara, dake Umudike, shine shugaban kungiyar asirin.

Ya kara da cewa Awom, dan wani boka ne kuma yace kisan wani ramuwar gayya ne akan kisan da aka yiwa tsohon shugaban kungiyar asiri na Burkina Faso.

XS
SM
MD
LG