Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhammad Ali Da Mike Tyson Ne 'Yan Damben Boxing Da Suka Fi Fice A Duniya


A duk lokacin da mutum ya budi baki ya yi tambaya akan shahararrun ‘yan wasan damben zamani koda mai amsa tambayar bai damu da kallon wasan damben boxing ba, da wuya kaji ya ambaci wani ko wasu daban baya ga Muhammad Ali da Mike Tyson.

Wadannan ‘yan wasa biyu sun shahara wajan iya dambe, kuma sun kasance sanannu a duk fadin duniya sakamakon irin bajintar da suka nuna a wannan sana’a ta su.

A bangaren suna da fice a duniya tsakanin ‘yan wasan biyu, Muhammada Ali ya kasance wanda yafi kowa suna a cikin ‘yan wasan damben boxing a duniya, kana na biye da shi kuma shine Mike Tyson kuma dukkan su ‘yan kasar Amurka ne.

Muhammad Ali ya yi suna a idan duniya kuma an sanshi da juriya da iya dambe wanda ya rike kanbin damben duniya duk a sanadiyyar kwarewar sa. Yayin da shi kuma Tyson ya dauki wannan kanbi yana da shekaru 20 da haihuwa, kana daga baya aka garkame shi a gidan kaso daga shekarar 1991 zuwa 1995 a sakamakon zarginsa da cin zarafin wata mata.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG