Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakamata Malamai Da Sarakuna Su Fadakar Da Jama'a Tanajin Addini Akan Kulla Da Yara


A shirinmu na mata, a yau na mussamam ne domin kuwa uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari ta sha alwashin daukar nauyin kula da lafiyar yaron nan mai suna Musa da kishiyar uwarsa ta lahanta shi.

Aisha Buhari dai tayi tir da mata masu ire iren wannan dabi’a , inda ta ke cewa tunda mahunkunta sun dauke nauyin karantun Musa zata dauke nauyin kula da bangaren lafiyarsa inda mahukuntan jihar Kano bazasu gacewar tayi shisshigi ba.

Ta kara da yin kira ga Malamai da Sarakuna da su fadakar da aluma bisa tanajin da addini yayi na cewa akalla a bar yaro a hannun mahaifiyar shi har na tsawon shekaru bakwai koda mahaifan sun rabu.

Shi dai wannan yaro mahaifiyarsa sun rabu da mahaifinsa sai aka baiwa kishiyar mahaifiyarsa nauyin kula da yaro, amma sai aka yi rashin sa’a maimakon baiwa yaro lura na hakika sai ta dauki gana masa ukuba a matsayin sana’a.

XS
SM
MD
LG