Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Haramta Ma Wata Uwa, Sama Jariran Ta Wani Suna!


twins
twins

Suna linzami! A cewar masu iya magana, akan lakama abu suna don asamu hanyar da za’a iya gabatar da wannan abun don fahimta ga mutane. A duk lokacin da aka haifi yaro ko jaririya a kowace kasa ko kuma kowace al’ada a duniya. Akan sama yaron ko yarinyar suna da za’a dinga kiran su da shi.

Amma akwai wasu sunannaki da suke da ma’ana wasu kuwa, sai dai a sasu don nishadi. Wata mata ta haifi tagwaye, ta kuma sa musu suna “Cyanide” da “Preacher” a nata tunanin cewar wai wannan sunan na Cyanide, sunan wani guba ne da yayi sanadiyar mutuwar tsohon shugaban soji na kasar Germany, “Hitler” da ministan shi “Joseph Goebbels” Ta kuma kara da cewar ai tana da hakkin sakama ‘yayan ta sunan da take so.

Amma alkali “Eleanor King” ta bayyanar da cewar wannan sunan kan iya zama wani abun damuwa ga yarinyar idan ta girma. Don haka ta hana uwar sama jaririyar wannan sunan. Ta kara da cewar idan yarinyar ta fahimci ma’anar sunan da cewar yana nuni da guba, to za’a iya samun sabani tsakani yarinyar da mahaifiyar ta a nan gaba. Mahaifiyar ta bayyanar da dalilin ta, na saka mata wannan sunan, da cewar anyi mata fyade ne aka samu juna biyu na yaran, don haka yasa zata sa wannan suna ga yarinya daya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG