Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bana Ba Dani Ba, A Wasan Zakaru Na "U.S Open"!


Shaharraren dan wasan kwallon rami “Golf” Tiger Woods, ya bayyanar da cewar ba zai samu damar halartar wasan zakaru na kasar Amurka “U.S Open”da za’a bude sati mai zuwa ba. Ya tabbatar da cewar yana samun sauki, amma haryanzu yana ganin cewar, bai samu saukin da yakamata ace ya koma fili ba.

Wannan gasar wasan kwallon ramin na “Quicken Loans National” na gidauniyar dan wasan ne Tiger, an ruwaito dan wasan Tiger, na cewa a shafin shi na yanar gizo “Duk dai da cewar ina kara samun sauki, amma ban tsanmani cewar nakai dai-dai lokacin da ya kamata ace na fara buga wasa ba.”

Sai ya kara da cewar, “Ina kara mika godiya ta, ta musamman ga masoya na, da goyon baya da addu’ar samun lafiya. Ina samun sakonnin email, da na gaggawa, daga mutane, nagode kwarai da gaske.” Ya kara da cewar yana yima abokan shi Mike Davis, da Diana Murphy, fatan alkwairi a wannan kakar wasan da zasu fara.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG