Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gargadin Watan Ramadana


Yau mun sami bakuncin Malam Usman Shehu Muhammad wanda yayi mana huduba da gargadi domin gujewa aikata ayyukan da basu dace ba wadanda subuhanahu wata;ala ya la'anta da kuma sa hukunci mai tsanani akan masu aikata irin wadan nan laifuka.

A yau malamin ya yi jawabi ne akan laifin ZINA! malamin ya ce "ZINA masifa ce wadda duk al'umar da ta afka ciki to ta lalace kuma ta shiga uku, kuma bata dawowa cikin hayyacinta sai ta tuba ta daina.

Shiyasa kira na ga maza da mata wadanda suka san suna zaluntar kawunansu, kuma suna zalumtar wannan al'umma suna aikata wannan mugun aiki da su tuba ga Allah madaukakin sarki, su kuma taimakawa wannan al'uma su daina wannan aiki domin Allah ya jikan mu duka.

Tarihin duniya ya nuna duk al'umar da take aikata wannan Allah ba ruwan shi da ita!, duk al'umar da take zina Allah kyale ta yake domin abokan gabarta suyi ragaraga da ita, su yi yadda suka ga dama da ita tamkar irin yanayin da muke ciki yanzu"

Ga cikken gargadin.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG