Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wanene Dan Wasan Da Yafi Kowanne Dan Wasa Samun Kudi a Duniya?


Cristiano Ronaldo

Fitatciyar muhajjar nan ta Amurka Forbes ta fitar da sunan Christiano Ronaldo a matsayin dan wasa namiji da yafi sauran ‘yan wasan samun kudi a Duniya.

Ronaldo shine dan wasan kwallon kafa na farko da aka taba fitar da sunansa a matsayin wanda yafi kowanne dan wasa samun kudi.

Cikin watanni 12 da suka gabata Ronaldo ya sami kudi wuri na gugar wuri har Dala Miliyan 88, hakan na nufin ya wuce Lionel Messi wanda yazo na biyu da Dala Miliyan 6.6

Wannan shine karon farko da wani dan wasa idan aka cire Tiger Woods da Floyd Mayweather ya taba shiga jerin sunayen.

Serena Williams yar wasan Tennis tazo ta 40 a jerin sunayen, duk da haka itace tazo ta farko a mata, takwararta ‘yar kasar Rasha Maria Sharapova tazo ta 88. Su biyu ne cikin mata sunayensu ya fito a jerin.

Mujallar Forbes dai ta lissafa dukkan hanyoyin da ‘yan wasan ke samun kudinsu daga 1 ga watan Yuni na shekarar 2015 zuwa 1 ga watan Yuni na shekarar 2016.

XS
SM
MD
LG