Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kafin Keshi Ya Mutu An Shirya Zai Gana Da Jami’an Kasar Guinea Kan Maganar Aiki


Stephen Keshi

Kafin Stephen Keshi ya mutu an shirya cewar zai gana da jami’an hukumar kwallon kafar Guinea a yau Laraba, Kwasam Allah ya dauke ransa awanni kafin wannan ganawa.

An dai fitar da rahotan cewa tsohon koch din na Super Eagle ya rasa ransa ne a birnin Benin, inda aka ce bugun zuciyane sanadiyar hakan.

Wani dake kusanci da Stephen Keshi ne ya fadawa shafin AfricanFootball.com cewar, an shirya Keshi zai gana da wasu jami’an hukumar kwallon kafar Guinea a jihar Lagos yau Laraba kan maganar aiki.

Keshi dai yayi aiki da kasashe rainon Faransa dake nahiyar Afirka, a lokacin da ya samu damar zuwa wasannin cin kofin shekara ta 2006, ya karbi jagorancin kasar Mali tsakanin shekara ta 2008 da 2010.

Kasar Guinea dai na niyyar maye gurbin Lius Fernandez da Stephen Keshi.

XS
SM
MD
LG