Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dakatar Da Sharapova Na Shekaru 2, Zata Rasa Dalla Milliyan $50!


A jiya Laraba ne, kwamitin kasa-da-kasa na masu wasan kwallon “Tennis” suka bayyanar da sakamakon binciken su, inda suka dakatar da shahararriyar ‘yar wasan nan ta duniya Maria Sharapove, na tsawon shekaru biyu 2.

Hakan dai ya biyo bayan wani rahoto da ya bayyanar da ‘yar wasan ta sha wasu kwayoyi gabanin wasan da aka buga na Australia Open, a shekarar da ta gabata. 'Yar wasan mai shekaru ashirin da tara 29, tana ganin wannan matakin yayi tsauri, don haka zata daukaka kara akan matakin.

'Yar wasan dai, ta zama mace da ta kwashe kimanin tsawon shekaru goma sha daya 11, a matsayin mace da tafi daukar albashi mai tsoka a fadin duniya. Kamin ‘yar wasa Serena Williams, ta kwace kambun a shekarar da ta gabata. Domin kuwa ta samu kudi da suka haura dallar Amurka milliyan dari biyu da tamanin da biyar $285M. Daidai da naira billiyana hamsin da bakwai. Yanzu haka dai, idan har wannan dakatarwar ta tabbata, za’a ci ta tarar kimanin dallar Amurka milliyan hamsin $50M.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG