Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Stephen Keshi Kan Sabuwar Tawagar Super Eagles


Stephen Keshi
Stephen Keshi

A jiya Asabar ne Stephen Keshi yace kungiyar Super Eagles na bukatar lokaci kafin su kai ga inda ake tsammanin su.

Keshi yayi wannan furuci ne alokacin da yake zantawa da manema labaru bayan nasarar da kungiyar ta samu a wasansu da kasar Chadi inda aka tashi biyu da nema, ya kuma kara da cewa ya amince kungiyar zata yi abin kirki nan gaba.

“bawai muna yin uzuri bane, amma abinda dubawa anan shine sabbin ‘yan wasa ne a wannan tawagar, dolene sai munyi wasa gaba ‘dayan mu na wani ‘dan lokaci kafin mu fara yin yadda ya kamata. Amma ina da kwarin gwiwa akan wannan tawagar, kuma gaba ‘dayan mu zamu ci gaba da gina ta har sai takai matsayin yadda muke son ta.” Inji Keshi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya wato NAN ya fitar da rahotan cewa Super Eagles batayi kokari ba a farkon wasan wato kafin hutun rabin lokaci, amma ta farfado inda ta samu nasarar lashe wannan wasan na share fagen wasan cin kofin nahiyar Afirka.

Kokarin da yan wasan sukayi bayan da wowa daga hutun rabin lokaci shine yayi sanadiyar samun wannan maki ga kungiyar Super Eagles a filin wasan Ahmadu Bello.

XS
SM
MD
LG