Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sami Khedira Ya Koma Juventus


Sami Khedira celebra con Per Mertesacker el tercer gol que le dio a los alemanes la medalla de bronce en el Mundial de Sudáfrica.
Sami Khedira celebra con Per Mertesacker el tercer gol que le dio a los alemanes la medalla de bronce en el Mundial de Sudáfrica.

A kokarin da kungiyar Juventus ke yin a ‘kara karfin ‘yan wasan ta ‘dauki tsohon dan wasan Real Madrid kuma zakaran gasar cin kofin duniya ‘dan asalin kasar Germany Semi Khedira.

Zakaru Italiya sunce, Khedira mai shekaru 28 da haihuwa ya amince da kwantiragin shekaru hudu da Juventus.

Khedira, wanda aka sani da gudu da kwallo ta gaban masu tsaron gida kuma wanda ya iya sarrafa kwallo, da bajintar juya tamaula har ma da mika kwallo, Allah yayi masa basira ganin wasa. Inji Juventus

Bayan shigar sa kungiyar Real Madrid da ga Stuttgart a shekara ta 2010, ya buga wasa mai kyau na tsawon shekaru biyar a kulub ‘din da ke buga La Liga amma bai samu nasara ba bayan da akayi maganar ‘kara tsawon kwantiraginsa.

A watan daya gabata ne ya zargi kungiyar Real Madrid da cewar duk da yana cikin koshin lafiyar da zai iya buga wasa amma suka ajiyeshe gefe daga bugawa kungiyar wasa.

Tun daga wannan lokaci bai yi wani tasiri ba har na tsawon shekara, Real Madrid dai tace dalilin jin ciwo ne yasa bai buga wasan ba, amma Khedira yace kungiyar dai bata bukatar sa ne kawai.

XS
SM
MD
LG