Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Super Falcon Sunyi Kunnen Doki


Kwallon mata
Kwallon mata

A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya na mata da ake gudanarwa a kasar Canada, Najeriya, da kasar Sweden sunyi karon batta jiya litinin inda aka tashi wasan kunnen doki ukku da ukku.

Kasar Sweden, dai ita ta fara jefa kwallo a ragar ‘yan Najeriya, a rukuninsu na D, wanda akewa lakabi da rukunin mutuwa, inda daga bisani suka jefa kwallaye ukku.

Da aka dawo hutun rabin lokaci Ngozi Okobi da Asisat Oshoala da kuma Francisca Ordega, sun yi abun bajinta domin sun samu jefa kwallaye ukku wanda ya baiwa Najeriya damar yin kunnen doki da Sweden.

Ita kuwa kasar Amurka, ta lallasa kasar Australia, da ci ukku da daya, a wasa na biyu da aka buga a rukunin D, a zagayen wasansu na biyu ranar Juma’a Amurka, zata hadu da kasar Sweden ko yaya wannan wasa zai kaya .

XS
SM
MD
LG