Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Stephen Keshi Kan Maganar John Mikel


Coach Stephen Keshi speaks to members of the Super Eagles at practice in Abuja before their World Cup qualifier against Ethiopia.
Coach Stephen Keshi speaks to members of the Super Eagles at practice in Abuja before their World Cup qualifier against Ethiopia.

Babban kochin kungiyar Super Eagles Stephen Keshi ya bayyana wa manema labarai dalilin sa barin ‘dan wasan Chelsea John Mikel da kuma mai tsaron gida Austin Ejide daga tawagar kungiyar, wanda zasu kara da kasar Chadi a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Alokacin da Stephen Keshi ke magana da ‘yan jarida, a jiya Asabar ya musanta zargin da ake na cewa yana da matsala Mikel Obi, ya kuma ce yayi magana da Mikel akan rashin saka shi cikin ‘yan wasan na Super Eagles.

Yace, “na yanke shawarar ba zan kawo tawagar ba a yanzu, saboda bana bukatarsa kuma munyi magana aka, ya kuma ce babu matsala. Na gaya masa cewa zamuyi magana akan wasa mai zuwa na watan Satumba.”

Keshi ya cigaba da cewa akan mai tsaron gida Ejide kuwa, zamuyi wasa ‘daya ne kawai da kasar Chadi. Don haka kawo masu tsaran gida har biyu da suke wasa a kasashen waje bashi da ma’ana, ina tunanin baiwa ‘yan wasan cikin gida damar zuwa da kaftin Enyeama.

Idan da wasanni biyu zamuyi to babu damuwa, da na hada da Mikel da Austin Ejide.

Masu tsaron gida uku da muke da su yanzu a sansanin horon mu, sun ishe mu a wasan da zamu buga. Idan bamu basu dama yanzu ba yaushe zasu zama kamar su Ejide ko Vincent Enyeama ko Emmanuel Okala?

XS
SM
MD
LG