Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Issa Hayatou na Cikin Masu Kwadayin Kujerar Sepp Blatter


A bayan da haka kwatsam Sepp Blatter yace zai sauka daga kan mukamin shugaban hukumar kwallon kafar duniya ta FIFA, masu kwadayin kujerar yanzu sun fara daura aniyar fafatawa.

Tun kafa hukumar FIFA a shekarar 1904, mutane 9 kawai suka taba rike kujerar shugabancinta. A shekaru 40 da suka shige kuwa, mutane biyu ne rak suka hau kan wannan kujera, watau Joao Havelange dan kasar Brazil daga 1974 zuwa 1998. Sai kuma Sepp Blatter daga 1998 har zuwa yau.

Daga cikin wadanda ake rade-radin cewa suna kwadayin wannan kujera har da Issa Hayatou, mutumin da tun shekarar 1988 yake shugabancin hukumar kwallon kafa ta kasashen Afirka CAF, wanda kuma a 2002 ya kalubalanci Sepp Blatter wajen zaben shugabancin FIFA amma ya sha kashi.

Shi ma shugaban hukumar kwallon kafar kasashen Turai ta UEFA, Michel Platini, yana kwadayin kujerar ta Blatter domin ya so ma ya kalubalance shi a zaben da ya shige, amma sai ya fasa.

Yarima Ali na kasar Jordan shine yayi takara da Blatter a makon da ya shige, kuma la shakka zai sake neman wannan kujera. Yarima Ali, mai shekaru 39 da haihuwa, shine matashi mafi karancin shekaru cikin wadanda suak nemi kujerar ko suke son nema a yanzu.

A karshe, akwai Michael van Praag dan kasar Holland wanda an zabe shi ya tsaya takarar da Blatter, amma sai ya janye ya bayyana goyon baya ga Yarima Ali.

Ana sa ran hukumar ta FIFA zata gudanar da zabe tsakanin watan Disambar bana zuwa watan Maris na shekara mai zuwa domin zaben wanda zai gaji Blatter.

XS
SM
MD
LG