Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban FIFA Yayi Murabus


Washington, DC -- Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, Sepp Blatter, yayi murabus haka kwatsam a yau talata a tsakiyar wani abin fallasa na almundahana a hukumar.

Kwanaki hudu kacal da suka shige aka sake zaben Blatter a matsayin shugaban hukumar FIFA. Yayi kiran da a gudanar da taron gaggawa na hukumar kwallon kafar domin zaben wanda zai gaje shi, ya kuma ce zai ci gaba da zama kan kujerar har zuwa lokacin da za a samu magajinsa.

Sai dai kuma zai dauki watanni kafin a gudanar da zaben sabon shugaban hukumar ta FIFA. Masu kula da sha'anin hukumar ta FIFA sun ce watakila sai a tsakanin watan Disambar wannan shekara zuwa watan Maris na 2016 za a iya gudanar da zaben sabon shugaba.

XS
SM
MD
LG