Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Goyon Bayan ya Hau Shugabanci


Hukumar kwallon kafa ta kasar Amurka, ta janye goyon bayan da takewa shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Sepp Blatter, gabanin zaben shugabancin hukumar ta FIFA, da za’a gudanar yau a Zurich ta kasar Switzerland.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Amurka, Sunil Gulati, kuma daya daga cikin jami’in hukumar FIFA, yace tun kafin wannan badakalar ta fito ya nuna a fili cewar yakamata a takawa Sepp Blatter, birki.

Yanzu da guguwar almundahana a kan hukumar ta FIFA, Gulati, na kai gwauro da mari domin ganin cewa Amurka ta goyi bayan Yerima Ali bin Hussein wanda ke takara da Blatter.

Gulati, yace Yerima Ali bin Hussein, ya taka rawar ganin a hukumar kwallon kafa ta kasar Jordan kuma yana zammar kawo sauyi mai ma’ana kamar yanci mata da na matasa.

XS
SM
MD
LG