Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hazard Yayi Kira Ga Benteke Yazo Chelsea


Football - Chelsea v Sunderland - Barclays Premier League - Stamford Bridge - 24/5/15Chelsea's Eden Hazard celebrates with team mates after winning the Barclays Premier LeagueAction Images via Reuters / Adam HoltLivepicEDITORIAL USE ONLY. No use with unau
Football - Chelsea v Sunderland - Barclays Premier League - Stamford Bridge - 24/5/15Chelsea's Eden Hazard celebrates with team mates after winning the Barclays Premier LeagueAction Images via Reuters / Adam HoltLivepicEDITORIAL USE ONLY. No use with unau

Dan wasan kugiyar Chelsea Eden Hazard, ya nuna cewar yana matukar son ace takwaransa ‘dan wasan Belgium Christian Benteke zai dawo kulub din Chealse a wannan kakar wasan mai zuwa.

Ana alakanta ‘dan wasan na Aston Villa Christian Benteke da kungiyar Chelsea, Manchester United da Liverpool, kuma bayanai na nunin cewa farashin da aka saka masa yakai kudin yiro milayan 32.5

Didier Drogba yayi wasan sa na karshe da kungiyar Chelsea, Jose Mourinho saka ido kan sabon da wasan da zai sayo kafin kakar wasa mai zuwa. Hazard dai na fatan takwaran nasa zai dawo Chelsea, ya kuma fadawa manema labarai cewa “Idan har Christian yazo kulub din mu to zan zama mutumin da yafi kowa farin ciki a duniya.”

Ya ci gaba da cewa ina da dangantaka mai kyau da shi, kuma babu abinda yafi yin wasa tare da shi dadi. Shekarar Chritian 25, yana cikin shekarun da zai yiwa kansa zabi mai kyau a rayuwar sa.

Hazard wanda ya bugawa kulub ‘din sa da kasarsa wassani sama da hamsin a wannan kakar wasan, ya kuma ce zai so lokacin tafiyar sa hutu yazo bayan wahalar da ya sha wajen neman zama zakaran wasa na wannan shekarar.

XS
SM
MD
LG