Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mourinho ya Karyata Labarin Jita-Jita Cewar!


Chelsea ta doke kungiyar kwallon kafa ta Sydney da ci daya mai banhaushi a wani wasan sada zumunta, a jiya.

Bayan wannan nasarar da Chelsea ta yi na doke Sydney, Koch din ta Jose Mourinho, ya karyata labarin jita-jitar cewa Diego Costa, na neman barin kungiyar ta Chelsea.

Fitatcen dan wasan dai daga Real Madrid, yayi kaura zuwa Stamford, gabanin kakar kwallon shekarar 2014, zuwa 2015, inda yayi rawar gani da jefawa Chelsea, kwallaye 20 a, raga.

Amma akwai rade-radin dake cewa Diego Costa, ya gaji da zaman Ingila, saboda haka yana neman hanyar komawa kasar sa ta Spain.

Mourinho, yace Chelsea, wurin zaman Costa ne domin shine ke gudanar da abubuwan da yakamata a kungiyar kuma ya kasance mai jin dadin zama a kungiyar Chelsea.

XS
SM
MD
LG