Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Super Falcons Na Shirin Karon Batta Da Australiya


kwallon mata
kwallon mata

A daren yau jumma’a ne ‘yan wasan Super falcons na Najeriya zasu yi arangama da ‘yan wasan kasar Australiya a filin gasar cin kofin kwallon kafar mata ta duniya a garin Winnipeg a Canada.

Kowaccensu, tana bukatar lashe wasan nayau a rukuninsu na D, inda su biyun suke kasan sauran kasashen dake wannan rukunin. Amurka, wadda zata kara da kasar Sweden daga baya a yau din, itace take saman rukunin da maki 3 bayan da ta doke Australiya a wasan farko. Sweden da Najeriya da suka yi kunnen doki, suna da maki daddaya, kuma suna biye ma Amurka, yayin da Australiya take kasa ba ta da maki ko daya.

Idan matan Super falcons na Najeriya suka lashe wasan yau, zasu kasance suna da maki 4 ke nan, kuma tana kara ingiza su zuwa ga zagaye na biyu, yayin da watakila Australiya ba zata kai labara ba. Amma idan Australiya ta lashe wasan, Najeriya ta shiga cikin kasadar fita daga wasan baki daya saboda wasanta na karshe a rukunin zata yi ne da Amurka wadda take kan gaba a rukunin.

Masana tamaula sun ce idan har kwararrun ‘yan wasan gaba da Najeriya ke da su suka nuna hazakar da ta kamata, Najeriya na iya doke Australiya cikin sauki. Babban raunin ‘yan Najeriya shine rashin masu tsaron baya sosai.

XS
SM
MD
LG