Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Sai Super Falcons Sun Ci Wasan Su Da Amurka


Super Falcons
Super Falcons

Har yanzu dai kungiyar wasan mata ta Super Falcons bata ci wani wasa ba a wasan da ake na cin kofin duniya na FIFA, bayan da suka sha kashi da ci 2-0 a hannun Australia ranar juma’a.

Yar wasan Australia Kyah Simon ta zarga kwallo kafin hutun rabin lokaci da bayan hutun rabin lokaci, ‘yan matan dai sun farfado ne daga cin da Amurka tayi musu na 3-1 a wasan farko na gasar.

Gaba daya kungiyoyin dai na wasa ne tsakaninsu da juna karon farko gasar, amma ‘yan Najeriya sun yi wasa mai kyau.

Yan zu dai kungiyar Falcons na bukatar samun nasara a wasan karshe na rukunin su, wanda zasu buga da Amurka indan har suna son su wuce gaba a gasar cin kofin duniya na mata FIFA.

XS
SM
MD
LG