Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Seun Kuti Yayiwa Buhari Murna Da Kuma Kira Ga Matasan Najeriya


Seun Kuti, son of Afrobeat music legend Fela Kuti, performs at "Felabration," an annual event paying homage to his father, at the New Afrika Shrine in Lagos, Oct. 20, 2013.
Seun Kuti, son of Afrobeat music legend Fela Kuti, performs at "Felabration," an annual event paying homage to his father, at the New Afrika Shrine in Lagos, Oct. 20, 2013.

‘Dan shahararran mawakin nan Fela Kuti, Seun Kuti, wanda shine ya gaji mahaifinsa a fagen waka, ya yiwa janal Muhammadu Buhari murnar nasarar lashe zaben shugaban kasa da akayi na ranar ashirin da takwas ga watan Maris.

Shi dai Seun, na daya daga cikin mutanen dake hamayya da tsohon shugaban mulkin soja janal Buhari, saboda yana zargin Buhari da kone gidan mahaifinsa.

Mawakin dai yakuma nuna jin dadin sa ga tsohon gwamnan Lagos, Bola Tinubu saboda kokarin da yayi na ganin an kawo canji a Najeriya. Ya kuma yabawa matasan Najeriya, da cewa sune suka kawo wannan canji kasar, harma ya shawarcesu da goyi bayan gwamnati mai zuwa domin samun amfani ga kowa.

Daga karshe yace mu matasan Najeriya, kada mu kwanta barci yanzune lokacin da zamu tashi tsaye don ganin gwamnati tayi aiki, kuma mun sami cigaba.

XS
SM
MD
LG