Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kungiyar Matasan Najeriya (NYO), Abubakar Dangulguli Ya Shawarci Matasa Kan Da'a Da Natsuwa


Matasa cikin kwanciyar hankali
Matasa cikin kwanciyar hankali

Shugaban kungiyar Matasan Najeriya na Kasa, NYO a takaice, Alhaji Abubakar Dangulguli ya yaba da da’a da kuma natsuwar da matasan Najeriya su ka nuna a lokutan zaben Shugaban Najeriya. Y ace a baya duniya ta dauka Najeriya za ta wargaje sanadiyyar wannan zaben, sai gas hi an gudanar da komai cikin nasara saboda irin hadin kan da matasan bangarorin Najeriya su ka bayar.

To saidai kuma, Shugaban na matasa, ya yi Allah wadai da wace gona da irin da y ace wasu matasan na yi a yayin shagulgulan nasarar wannan zaben. Y ace da al’ada da addini da ma duk wata ka’dar rayuwa ta hana daukar mataki mai cike da hadari da sunan bayyana murnar wani al’amari. Don haka ya yi kira ga matasan Najeriya da su yi komai cikin natsuwa saboda a ci gajiyar dimokaradiyyar da su.

Shugaban na matasa ya kuma yaba ma sauran kungiyoyi n sa kai da na addinai da ma su shugabannin kungiyoyin matasan saboda jajircewar da su ka yi wajen ganin an yi komai cikin lumana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:53 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG