Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Kira Ga Buhari Ya Sake Farfadowa Da Fagen Wasa


'Yan wasan Najeriya Ogenyi Onazi da Joseph Yobo ke lailaye wani san wasa
'Yan wasan Najeriya Ogenyi Onazi da Joseph Yobo ke lailaye wani san wasa

Shugaban Kungiyar Marubuta Labaran Wasanni ta kasa, Alhaji Sa’idu Abubakar ya yi kira ga Shugaban Najeriya mai barin gado Janar Muhammadu Buhari (murabus) da ya saka bangaren wasanni cikin sassan da zai masu garanbawul sosai.

Alhaji Saidu Abubakar ya ce saboda muhimmancin da Buhari ya bai wa bangaren wasanni, a zamanin gwamnatinsa ta soji, har sai da aka cicci kofuna da sauran kyaututtuka da dama a zamanin gwamnatinsa ta soji. Ya ce a lokacin har sai da shugaba Buhari y aba da umurni kan irin abubuwan da yak e ganin ya kamata a yi a bangaren na wasanni to amma barinsa mulki ke da wuya abubuwa su ka sukurkuce. Aka ki amfani da ka’idojin.

Shugaban na ‘yan jarida marubuta labaran wasanni, ya yi kira ga Buhari da ya bullo da wata ka’ida wacce za ta ceto bangaren wasanni zuwa darajarsa ta zamanin mulkin sojin Buharin. Ya ce lallai kam ya kamata a farfado da fannin wasanni saboda akwai matasa da dama da za su iya sake daga darajar Najeriya a fannin wasanni kamar yadda abun ya ke a baya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:25 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG