Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Bom Na Farko Bayan Zaben Shugaban Kasa A Najeriya


Fashewar bom a kasuwar birnin Bauchi.
Fashewar bom a kasuwar birnin Bauchi.

Rahotanni daga jihohin Bauchi da Gombe na bayanin cewa anga wasu ‘yan bindiga a cikin motoci suna ratsa garuruwan Futuk da Digare a jihar Bauchi, sai kuma garuruwan Kashare, Funduga da kuma Tumu a jihar Gombe.

Wani mazaunin daya daga cikin garuruwan ya shaidawa wakilin mu Abdulwahab Muhammad, cewar ‘yan bidigar basu harbi kowa ba saidai suna ta kabbara suna tafiyar su. Saidai bincike ya nuna ‘yan bindigar basa cikin yanayi mai kyau, da alamu yunwa ta galabaitasu suna ta gararanba ne a cikin daji.

Ana cikin wannan yanayi ne aka samu labarin an tada bom a kofar tashar mota, mai suna tashar motar Bauchi, dake garin Gombe, shedun gani da ido sunyi bayanin cewar a kalla mutane biyar ne suka mutu dayawa sun sami rauni.

Wannan dai shine karo na farko da aka samu tashin bom, tun bayan da aka gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya.

XS
SM
MD
LG