Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Fulani Sun Yabawa Shugaba Jonathan


Matasan Fulani a Najeriya, sun yabawa shugaban kasa mai barin gado Goodluck Jonathan, a game da barkar da yayiwa shugaban kasa mai jiran gado janal Muhammadu Buhari.

Alhaji Shu’aibu Haruna Sogiji, shugaban kungiyar matasa ta Fulani a Najeriya, wanda yace ya jinjinawa shugaban kasar Najeriya, da fitowa kafin ma a sanar da sakamakon zabe ya fito ya yiwawa janal Buhari murnar nasarar lashe zabe, ya kuma yi kira ga duk shugabannin Afirka da suyi koyi da yadda shugaba Goodluck Jonathan yayi.

Sogiji, ya nuna farin cikin sa da ‘yan Najeriya suka zabi Janal Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya. Shugaban kungiyar Fulani matasan dai yayi wannan kira da yawun duk ‘yan kungiyar matasan Fulani na Najeriya.

XS
SM
MD
LG