Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Zata Kashe Fam Miliyan £160 Wajan Sayen 'Yan Wasa Biyu


A yayin da aka shiga hada hadar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa na duniya, Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, mai rike da kambun laliga na kasar Spain, a bana ta ware fam miliyan £160 wajan sayen 'yan wasa biyu kacal.

'Yan wasan sune Eden Hazard, na Chelsea, wanda ta ware masa fam miliyan 100 sai mai tsaron raga na Manchester United, David De Gea, wanda a ka ware masa fam miliyan £60.

Sai dai kungiyar Manchester United, tayi watsi da tayin da akayi wa dan wasantan na fam £60m.

Ita kuwa Manchester City, zata kashe sama da fam miliyan 50, don ganin ta sayo dan wasan baya daga Southampton, mai suna Virgil Van Dijk. Leicester city ta saka fam miliyan 50, ga duk kungiyar da take da sha'awar dan wasan Riyadh Mahrez,

PSG ta amince zata biya fam miliyan 60 domin sayen dan wasan gaba na kasar Gabon mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, Emerick Aubameyang.

Dan wasan gaba na Arsenal Lucas, Perez dan shekaru 28 da haihuwa yace yana da sha'awar barin kungiyar domin rashin samun kansa a wasannin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00



  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG