Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arsenal Da Chelsea Zasu Fafata A Wasan Karshe Na FA Cup


A yayin da aka kammala gasar Firimiya lig ta kasar Ingila ta shekara 2016/17

Yanzu hankali ya Koma kan wasan karshe na cin kofin kalu bale na kasar ta Ingila FA cup 2016/17

Ranar Asabar 27 ga watan Mayu na shekarar 2017 za'a buga wasan karshe tsakanin Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da takwararta ta Chelsea

Chelsea, dai ita ta lashe gasar Firimiya ta bana da maki 93
Ita kuma Arsenal, ta kare a mataki na biyar ne da maki 75 wanda hakan ya hanata zuwa gasar cin kofin zakarun turai na shekara mai zuwa 2017/18

Arsenal, ce ta biyu a kungiyoyin da suka fi lashe wannan kofin FA inda ta dauka sau Goma sha biyu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG