Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barcelona Ta Nada Sabon Mai Horar Da 'Yan Wasanta


Alexis Sanchez
Alexis Sanchez

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta bada sanarwar daukan sabon mai horar da ‘yan wasanta Ernesto Valverde, Wanda ya maye gurbin Luis Enrique.

Ernesto dai tsohon dan wasan gaba na Barcelona ne a shekarun da suka wuce, Asatin da ya gabata ne ya bada sanarwar ajiye aikinsa da kungiyar Athletic Bilbao, inda a yanzu ya amince zai rike kungiyar ta Barcelona na tsawon shekaru biyu.

Ita kuwa kungiyar Borussia Dortmund ta fidda sanarwar sallaman kocinta ne mai suna Thomas Tuchel dan shekaru 43 da haihuwa, Arsene Wenger ya Amince zai kara rattaba hannun a kungiyar sa ta Arsenal har na tsawon shekaru biyu mai zuwa.

Manchester United tana kan gaba wajan zawarcin dan wasan baya Danny Rose daga Tottenham.

Arsenal tace zata biya ‘yan wasanta Alexs Sanchez da Ozil fam miliyan 30 duk shekara a matsayin albashi in har ‘yan wasan sun amince da suci gaba da zama a kungiyar

Arsenal dai tana fuskantar barazana daga ‘yan wasan na barin kungiyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

XS
SM
MD
LG