Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Saurayi Ya Kai Karar Budurwar Shi Kan Dalilin...


Brandon Vezmar, mai shekaru 37, ya shigar da karar sabuwar budurwar shi, inda yake neman kotu, ta amsar mishi kudin shi kana kuma ta tura budurwar tashi gidan jarun. Yana karar budurwar tashi akan cewar ta bata mishi kudin shi.

Kwanaki kadan da suka hadu da wannan budurwar tashi, a shafin soyayyar yanar gizo, sun shirya zuwa silma, gidan kallo don samun fahimtar juna. Bayan sun isa gidan, ya biya kudin kallo dallar Amurka $17.31 dai-dai da naira 700.

Bayan sun shiga dakin kallo, sai budurwar tashi ta dauki wayar salular ta, tana catin da kawarta. A cewar Brandon, ta dauki kimanin mintoci 10-20 tana catin, daga bisanin ya cemata, ta tafita waje tayi magana idan tana da bukatar hakan, don damun su da take.

Daga fitarta bata sake dawowa ba, hakan ya bashi haushi, ganin cewar ta bata mishi kudin shi. Hakan yasa yake bukatar da ta biya shi kudin da ya biya na shiga silma, alhalin bata kalla fim din da ya biya kudin don shiba.

Budurwar tace, ai wannan hauka ne, ace saurayin nata ya kaita kara don wadannan kananan kudin. Ta kara da cewar a zahirin gaskiya, bata kwashe tsawon lokacin da yace tana magana ba, ta dai san da cewar tayi magana da kawarta.

Wadda take fuskantar matsala tsakanin ta da saurayinta, inda take kokerin bata shawara. Hattara dai ‘yan mata, masu bata kudin samarin su. Haka hattara matasa masu kokarin burge ‘yan mata.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG