Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ku Mike Mata Ba Rago Sai Malalaci - Inji Fadila Nuraddeen


Lokaci yayi da iyaye mata zasu karfafawa ‘yayansu mata gwiwar samun ilimin zamani da sana’oin dogaro da kai gami da ilimin addini domin samun wayewar zamantakewa inji matashiya Fadila Nurideen Muhammad.

Fadila ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da wakiliyar DandalinVOA, ta kuma kara da cewa karanci aikin jarida ne domin kuwa tun da ta tashi tana da sha’awar jin labarai da karance karance, malamar ta bayyana cewa tun tashinta tana sha’awar zama mai dogaro da kai domin gujewa sauyi irin na rayuwa.

Daga karshe ta yi kira ga iyaye da mata matasa cewar ya kamata mata sun san cewa koda kana da mai baka toh lallai wata rana lamarin na iya sauyawa.

Ta kuma bukaci iyaye su dinga baiwa mata damar kwatanta ayukan yau da kullum domin su sami kwarin gwiwar tsayawa kan kafafansu, domin babu rago sai malalaci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:44 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG