Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arsene Wenger Ya Bukaci A Saya Masa 'Yan Wasa Bayan Karin Shekaru Biyu A Kungiyar


A yayinda wasu magoya bayan kungiyar Arsenal, suke nuna rashin jin dadin yadda Maihoras da kungiyar Arsene Wenger, yake Jan ragamar kungiyar sai gashi a yau 31/5/2017 kungiyar ta Arsenal, ta bada sanarwar sake kara masa kwantirakinsa har na tsawon shekaru biyu inda zai kammala a shekara ta 2019.

Sai dai Wenger, ya umurci shuwagabanin na Arsenal su saya masa 'yan wasa kamar haka; Carlos Bacca na AC Millan da Reyad Mahrez na Leicester city da kuma dan wasan tsakiya na Monaco, wato Thomas Lemar, dan shekaru ashirin da daya da haihuwa.

Kungiyar ta Arsenal, ta amince zata bashi fam miliyan 100 domin yuwar hakan kafin a rufe saye da sayarwa na bana.

Shi kuwa dan wasan gaba na kasar faransa Antoine Griezmann, ya shaida wa kungiyarsa ta Atletico Madrid, cewar bazai zauna a kulob dinba
Manchester United, dai ta saka fam miliyan 87 domin ganin ta kawo dan wasan
an dai cimma yarjejeniyar kusan kashi 60/100 na dan wasan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG