Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kwallo Mafi Tsada A Duniya Paul Pogba, Yace Babu Gari Kamar Makka


Paul Pogba
Paul Pogba

A jiya ne shaharren dan wasan kwallon duniya, wanda yafi kowa tsada Paul Pogba, ya saka hoton shi a yayin da yake ibada, a masallaci mai tsarki a kasar Makka. Dan wasan ya ziyarci dakin Allah, ne don mika godiyar shi ga Allah, biyo bayan nasarar da ya samar ma kungiyar shi ‘yan kwanaki kadan da suka wuce.

Dan wasan da yake bugama klob din Manchester United kwallo, ya taka leda a lokacin wasan su na kawance kasashen turai ‘Europa League’ ya aika da sakon gaisuwa ga dukkan masoyan shi, a ko ina a duniya, da fatan ayi ibada lafiya a wannan watan mai albarka na Ramadan.

Ya rubuta a shafin shi na Instagram da cewar “Wannan guri shine guri mafi kyau da ya taba gani a rayuwa shi” yana nufi da cewar dakin Allah ‘Ka’aba’ mafi yawan musulamai a duniya sukan ziyarci kasa mai tsari a watan Azumi, don neman yarda Allah.

Ya saka hoton shi yana kusa da Ka'aba, bayan wani bidiyo da ya saka, wanda yake daukar masallacin a yayin da karatun Al-Kur'ani ke tashi a bayan bidiyon.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG