Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maryam Aminu Baba Tayi Fice a Faggen wake wake a tsawon rayuwarta


Maryam Aminu Baba Hassana

Allah ya yiwa Maryam Aminu Baba Hassan, rasuwa ta yasu ranar asabar a Kano, bayan wata 'yan gajeruwar rashin lafiya.

Maryam dai tayi fice a faggen wake wake a tsawon rayuwarta wanda ya kasance a cikin wake wakenta tayiwa Dandalinvoa da filin abari ya huce wakoki daban daban.

Irin wakokin da Maryam, ke rerawa suna hada da wakan sarakai da fitattun mutane a al'uma.

Dangane da batun fadakarwa kuwa da kuma kishin kasa Maryam, ta yi wakar fasa kwauri inda a cikin wakar ta nuna rashin alfanun kin biyan haraji kan kayayyakin da aka shigo dasu, ko kuma bita barauniyar hanya da kayayyaki.

Allah ya jikan Maryam yasa mutuwa hutu ne ya kuma yi mata sakaiya da Aljanna Firdausi, ya kuma sa mu cikin da imani.

Ana iya sauraren hiranta da Ibrahim Alfa Ahmed, a Dandalinvoa.com

XS
SM
MD
LG