Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Samari, Hunturu Na Hana Kwalisa Da Zama Majalisa?


Shirin samartaka na wannan makon ya sami zantawa da wasu samari matasa wadanda suka bayyana mana nasu ra'ayoyin kamar yadda 'yan mata suka bayyana nasu ra'ayin akan wanka da yamma a lokacin hunturu domin fita cikin unguwa inda suke zantawa da 'yan matan su.

Bisa ga dukkan alamu dai samari sun kware wajan dabarar sa kayan sanyi da sunan gaye, domin kuwa sun bayyana mata cewar suna da kayayyaki iri daban daban da suke sa wa domin fitar yamma.

Da muka nemi jin tabakin su dangane da wanka kuma, samarin sun bayyana cewa lallai kayan sawa kadai baza su hana a gane rashin wanka ba, dan haka wajibi ne saurayi yayi wanka domin koda kayan sawa saurayi matashi ya cika maimaitawa abokan sa na iya raina shi.

Daga karshe matasan sun bayyan cewa hunturu baya taba hana su zaman majalisa da kuma cigaba da neman 'yan mata. sai dai lokacin da suke dauka na zaman majalisa ne kadai ke raguwa.

Saurari cikakkiyar hirar a nan.. Dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG