Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zawarci Pep Guardiola Ko Ina Zai Koma


Kocin Bayern Munich Pep Guardiola, daga dukkan alamu yana shirin barin Bayern Munich, ana kuma harsashen cewa zai koma Manchester City, ne.

Kwantarakinsa sa zai kare a karshe wanna shekarar a Bayern Munich.

Da yake Magana da manema labarai Guardiola dan shekaru 44, ya ce a yanzu bani da amsan da zan baku amma sati mai zuwa zaku san amsan.

Tsohon mai kula da ‘yan wasan Bayern Munich Ottmar Hitzfeld, ya ce Guardiola, ya riga ya yanke shawarar daukar Manchester City.

Kocin Manchester City, mai ci yanzu Manuel Pelligrini, yana da sauran shekara daya da rabi, amma hukumomin Manchester City daga dukkan alamu ba zasu bari Guardiola, da suka dade suna farauta ya kubuce masu ba.

XS
SM
MD
LG