Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Sabon Shirin Kannywood "Tauraron Gobe"


Victor Olademeji Kannywood
Victor Olademeji Kannywood

A filin nishadi shirin namu na mussamam ne domin kuwa mun sami zantawa da wani jigo a harkar fim mai bada umarni tare da daukar hoto amma mai motsi, ba wani ba ne illa Victor Oladimeji.

Victor ya ce zasu fito da wani sabon shiri da suka yi wa suna Kannywood next movie star wanda zasu tara masu sha’awar shiga harkar fim inda zasu yi musu gwaje gwajen a fannoni da dama idan za’a dinga tace wa ana zubar da wadanda basu sami nasara ba.

Kuma a karshe mutane goma ne zasu sami nasara inda za’a ba da motoci biyu ga wadanda suka fi kowa kwazo baya ga samu musu gurbi a kannywood industry.

A fannin tsegumi kuwa a jiya lahadi ne aka kammala kalankuwar da gwamnatin jihar Kaduna ta shirya don karammawa mawakan Nijeriya.

XS
SM
MD
LG