Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Shekaru 38 Cikakken Wata Zai Sake Bayyana A Ranar 25


Wata
Wata

A tabakin Mr. Fred Espenak, na hukumar binciken sararin samaniya “NASA” ya bayyanar da cewar bisaga dukkan alamu ranar 25, ga wannan watan wanda yayi dai-dai da ranar Chrismas, ranar zagayowar haihuwar Annabi Isah (AS) wata zai fito a cikakken shi, hakan dai ya taba faruwa kimanin shekaru 38, da suka wuce.

A wannan ranar da misalin karfe 6:11am na assuba, wata zai cika kamar yadda yake bayyana a ranakun 13, 14, da 15 a kowane tsakiyan wata. Bisa ga dukkan alamu hakan ba zai sake faruwa ba har sai nan da wasu shekaru masu yawa idan mutun na da tsawon kwanaki.

Sun kara da cewar, fitowar watan cikakke zai haskaka ko ina wanda har ake ganin cewar wannan mutumin mai suna Santa, bisa ga al'adar kasar Amurka, da kanzo don raba kyauta ga yara a lokacin bukin kirismas ba zai bukaci fitila ba don tsabar haken watan. Watan dai zai cika a wannan ranar wadda take ranar 25 da aka kirata a matsayin ranar sanyi mafi karfi a tsawon watan. Baza’a sake samun rana mai irin wannan sanyin ba har sai ranar 28, na watan Satunba, a dai-dai lokacin da wata zai wuce inuwar wata duniyar, cikin jerin duniyoyi 7 da ake da su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG