Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester Za Ta Kashe Kudi Don Cin Gasar Badi


Louis van Gaal, Kocin Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester United
Louis van Gaal, Kocin Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester United

Kungiyar wasan kwallon kafa ta Manchester United tace za su kashe kudi don ganin sun hada tawagar ‘yan wasan da za su kara da fitattun kungiyoyin kwallon a gasar cin kofin nahiyar turai na kakar wasa mai zuwa.

Zasu yi haka ne bisa jaorancin mai horar da ‘yan wasa Louis Van Gaal na sama da rubi ashirin na kudin da sauran suka kashe a bara da yawansu ya kai Fam din Ingila Miliyan 150, bayan faduwar bazatan da suka yi da kasancewa a mataki na bakwai a shekarar 2014, wanda hakan ya hana su cancantar buga gasar cin kofin Zakarun Nahiyar Turan.

Kungiyar kwallon ta Manchester ta ja damarar dawowa ga gasar fitattun na Turai, tare da daga darajar kurwar masoyanta da kuma ta kasafin kudaden kashewar daukar nauyin kungiyar.

Mataimakin shugaban Manchester Ed Woodward yace, sun yarda da kwazon aikin Van Gaal, amma kungiyar kwallon Manchester din za ta zage damtsen ‘yan tawagarta wajen fuskantar cin lambobin yabo a kakar wasan badi.

XS
SM
MD
LG