Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chelsea Tayi Babban Kamu Daga Atletico


Chelsea
Chelsea

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta tabbatar da cewa Nathan dan wasan gaba na kungiyar Atletico ya rattaba hannu domin ya buga mata wasan.

Dan shekaru goma sha tara da haihuwa kuma dan asalin kasar Brazil, Nathan zai koma kungiyar Chelsea, ranar 1, ga wataYuli kasa da watani biyu nan gaba.

Nathan dai ya bugawa Brazil, wasa a matakin ‘yan kasa da shekaru sha bakwai da na kasa da shekaru ashirin inda ya jefa kwallaye biyar kuma ya samu kyautar wanda yafi taka leda a gasar.

Tun watan da ya gabata ne dai Chelsea ta fara zawarci Nathan, domin ya dawo kungiyar ta.

Bayan da aka kamala yarjejeniyar, Nathan yace yana farin cikin yin wasa a Chelsea Zakarun Ingila, da kuma fatan koyon don bunkasa wasa na.

XS
SM
MD
LG